Kungiyar Tottenham Hotspur, ta shiga zawarcin Kylian Mbappe daga Paris Saint-Germain.
Spurs na kallon Bafaranshen a matsayin wanda zai maye gurbin Harry Kane, wanda rahotanni suka ce, yana neman gida a Munich gabanin yuwuwar komawa Bayern.
A cewar Marca, Tottenham ce kungiya ta baya-bayan nan da ta nuna sha’awarta ta siyan Mbappe bayan da PSG ta bayyana siyar da shi.
Kungiyar ta Premier tana fatan za su iya samun ɗan wasan, kuma suna shirin tattaunawa da kulob din Ligue 1 da tawagar dan wasan.
Tottenham, duk da haka, dole ne ta yi yaƙi da Chelsea, Manchester United, Real Madrid da Saudi Arabiya don siyan dan wasan mai shekaru 24.
Shugaban PSG Nasser Al-Khelaifi ya amince cewa ba za su bar dan wasan ya tafi kyauta ba amma a shirye suke su ci gaba da rike shi, muddin ya kulla sabuwar yarjejeniya.