Tottenham ta yi nasarar cin Southampton 4-1 a wasan makon farko a gasar Premier League kakar 2022/23 da suka kara ranar Asabar.
Southampton ce ta fara cin kwallo ta hannun James Ward-Prowse a minti na 12 da fara tamaula.
Daga nan ne Tottenham ta farke ta hannun Ryan Sessegnon, sannan Eric Dier ya zura na biyu a raga.
Tottenham ta ci kwallo na uku, bayan da Mohammed Salisu ya ci gida, sannan Dejan Kulusevski ya ci na hudu a fafatawar.