Tottenham ta sa yi ‘yan wasan Juventus Dejan Kulusevski da Rodrigo Bentancur, yayin da Tanguy Ndombele ya koma Lyon a matsayin aro.
Dan wasan tsakiya na Uruguay Bentancur, mai shekara 24, ya koma kan fan miliyan 15.9 wanda zai iya tashi da fan miliyan 5 a kan yarjejeniyar har zuwa 2026.
Dan wasan gefe na Sweden Kulusevski, mai shekara 21, ya koma kan aro na watanni 18 kan fan miliyan 8.3 tare da zabin siya kan fan miliyan 29.2.
Dan wasan tsakiya na Faransa Ndombele ya koma Lyon daga Tottenham a matsayin aro, wanda shekaru uku suka rage masa a Spurs.
Ndombele, mai shekara 25, ya koma Tottenham ne a kan kudi Euro miliyan 60 (£53.8m).