Masu garkuwa da mutane sun sako tsohon sakataren hukumar kwallon kafa ta kasa, Alhaji Sani Toro.
Haka kuma an saki tsohon mataimakin tsohon kocin Golden Eaglets, Garba Yila da daya daga cikin abokansu Alhaji Isa Jah.
An yi garkuwa da mutanen uku ne a ranar Asabar bayan sun halarci daurin auren dan tsohon shugaban hukumar NFF, Aminu Maigari.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 150.
Sai dai an ce sun sami ‘yanci da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar Talata amma babu tabbas ko an biya wani kudin fansa kafin a sake su ko kuma a’a.