fidelitybank

Toshon kakakin Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya fice daga APC

Date:

 

 

 

 

 

Tsohon Mai taimakawa Gwamnan Jihar Kano a kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fice da ga jam’iyyar APC.

A yau Litinin ne dai Yakasai ya sanar da ficewar ta sa da ga jam’iyar a yayin taron manema labarai a Kano.

Ya ce ya ɗauki matakin barin jam’iya mai mulkin ne sabo da rashin cika alkawuran da ta yi wa al’ummar ƙasar nan.

Yakasai, wanda a ke yi wa lakabi da Dawisu, yace Jam’iyyar APC ta gaza sauke mafi yawa daga cikin nauye-nauyen data daukarwa ƴan Nijeriya, dama abubuwan da ya kamata a ce gwamnati ta yiwa al’ummar ta.

“Da ni a ka yi tallan jam’iyyar APC a dukkanin mafi yawa daga cikin jihohin Nijeriya , kuma mun yiwa al’ummar kasar nan alkawura. Amma ni da kaina na gamsu da cewa jam’iyyar ta gaza dauke alkawuran data yiwa yan kasa”. Inji Yakasai

Salihu Yakasai, wanda Gwamnatin Kano ta kora da ga mukaminsa saboda irin kalaman da yake yi na sukar gwamnatin tarayya, ya ce ya dade ya na fadawa gwamnatoci gaskiya tun lokaci da PDP ta ke kan mulki.

“Saboda irin matsalolin da ƴan ƙasar nan suke cikin na rashin tsaro, rashin baiwa yan kasa kyakykyawar rayuwa , sanya ƴan kasa cikin mawuyacin hali, da ma wasu matsalolin, shi ya sa na fice daga jam’iyyar APC a wannan rana”.inji Salihu Yakasai

Tanko Yakasai yace nan gaba kadan zai baiyana Inda zai koma domin cigaba da gwagwarmayar siyasa.

Sai dai kuma Salihu Yakasai ya yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa bashi dama ya hidimta wa Jihar Kano, inda ya ce alakar shi da gwamnan ta zama ta uba da ɗa.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp