fidelitybank

Tonon Asiri: Mun gano gwamnan Arewa da ya kwashe kudi Naira biliyan 60 – EFCC

Date:

Shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati ta EFCC a Najeriya, Abdulrasheed Bawa ya ce hukumar ta bankado wani gwamna mai ci na wata jihar Arewacin kasar da ya kwashi tsabar kudi har Naira biliyan 60 daga asusun jiharsa a cikin shekaru 6.

Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da take aike wa manema labarai na wata-wata mai taken “EFCC Alert”

Abdulrasheed Bawa ya yi wannan ikarin ne game da batun a wata hirarsa da mujallar da hukumar ta ke wallafawa, ya ce gwamnan da a ka gano na wata jiha ce da ke Arewa ta tsakiya ko da ya ke bai fadi sunansa ba.

Ya kuma ce, “Zan iya gaya muku a kyauta cewa, sabon sashen da muka bude kan leken asiri ya na aiki tukuru, kuma ya na bankado abubuwa da dama. Daya daga cikin su shi ne wani gwamna a wata jiha ta Arewa ta tsakiya, mun gano cewa cikin shekara Shida da su ka gabata (mutum daya) ya cire tsabar kudin da suka kai Nair biyian 60”.

“Muna kallon abubuwan da ya ke yi, kuma ina tabbatar muku cewa bayan mun kammala bincike, za mu sanar da ‘yan Najeriya kan abubuwan da mu ka yi a bayan fage game da laifukan da a ke aikatawa ta amfani da shafukan intanet”. A cewar Bawa.

Ya kuma kara da cewar, “Ya kasance tare da mu kwana biyu kuma an sake shi; Ana ci gaba da gudanar da bincike, amma muna yin taka-tsantsan da taka tsantsan, domin haka ba za a tuhume mu da yin shari’ar kafafen yada labarai ba. Ina tabbatar muku cewa muna aiki a kansu, ba ma son yin magana game da al’amuran da a ke bincike, kuma tabbas mun gayyaci tsohon gwamna (Lucky Igbinedion), domin yi masa tambayoyi shi ma”. inji Bawa

thisday nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp