fidelitybank

TNM ta amince da shiga sabuwar jam’iyyar NNPP

Date:

Ƙungiyar siyasar nan mai suna The National Movement (TNM), wacce tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya kafa kwanan nan, ta amince da shiga sabuwar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Da yake jawabi bayan wani taro na sa’o’i bakwai a Abuja, shugaban riko na TNM na kasa, John Chris Ifeimeje, ya ce, kungiyar ta yanke shawarar daukar jam’iyyar NNPP ne, domin ceto kasar nan daga mummunan shugabanci da jam’iyya mai mulki ta shirya.

An kuma nada Ifeimeje a matsayin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar NNPP. Ya nada tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Buba Galadima a matsayin wani bangare na kwamitin riko.

Mambobin sun hada da Dr Boniface Aniebonam a matsayin shugaban kwamitin amintattu (BoT); Sanata Suleiman Hunkuyi, mataimakin shugaba; Hon. Oladipo Olayoku, Sakataren kasa; Major Gilbert Agbo, Sakataren Yada Labarai na kasa; da Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali, sakataren kungiyar na kasa; da sauransu.

A cewarsa, kungiyar tun bayan kaddamar da kungiyar a watan da ya gabata, ta samu gagarumin martani daga sassa daban-daban na kasar, kuma dimbin jama’a da kungiyoyi sun yi ta tururuwa zuwa sakatariyar TNM ta kasa, domin tantancewa da shiga kungiyar.

Ya kara da cewa jam’iyyar ta tsayar da ranar 30 ga watan Maris, domin gudanar da babban taronta na kasa.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp