fidelitybank

Tirƙashi: Ƴan bindiga sun sace Kwamishina yaɗa labaran jihar Binuwai

Date:

Gwamnatin jihar Benue ta tabbatar da sace kwamishinan yaɗa labarai da al’adu da yawon shaƙatawa, Matthew Abo da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ukum, Iorwashima Erukaa.

Babban Sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Tersoo Kula, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da Abo a gidansa da ke Sankara da misalin karfe takwas na daren Lahadi, yayin da aka yi garkuwa da Erukaa a ranar Asabar.

“Ƴan bingidar da suka yi garkuwa da mutanen biyun da har yanzu ba a san inda suke ba, sun tuntubi iyalan Erukaa amma har yanzu ba su tuntubi dangin Abo ba,” in ji sanarwar.

“Gwamnan wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin Allah-wadai kuma abin da ba za a amince da shi ba, tuni ya umarci hukumomin tsaro da su fara aiki nan take domin ganin an sako mutanen biyu cikin koshin lafiya.”

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, domin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin jihar ta kasance mai aminci ga kowa.

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp