Kamfanin Mai na ƙasa NNPCL, ya kara fitar da sabon farashin litar man fetur a Legas inda ya karu zuwa Naira 1,025, yayin da Abuja Naira 1,050 duk lita.
Ƙarin farashin na zuwa yayin da ƴan Najeriya suka ƙauracewa sayan mai saboda tsadar da yayi tare da samun raguwar ababan hawa dake sufuri a biranan ƙasar.
Har wa yau ƙarin na zuwa yayin da wasu Alƙaluman da hukumar kula da albarkatun ruwa da kuma ƙarƙashin ƙasa a Najeriya suka nuna cewar an samu raguwar man da ake sha daga lita miliyan 60 a kowacce rana zuwa lita miliyan 4 da dubu 500 a 20 ga watan Agustan 2024.
Makonni uku da suka wuce, a ranar 09/10/2024, kamfanin mai na NNPCL ya kara farashin litar fetur daga Naira 897 a Abuja zuwa Naira 1,030 yayin da ya kai litar fetur din Naira 998 daga tsohon farashin Lagos din na Naira 885
Jaridar Daily Trust ta ce, karin farashin da aka yi shi sau biyu cikin makonni uku ya biyo bayan daina biyan tallafin Naira 133 da NNPCL ke yi kan kowace litar fetur da aka sha a Nijeriya.