‘Yan bindiga da yawansu ya kai 100 sun farmaki wasu garuruwa a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja.
Gidan talabijin na Arise ya rawaito cewa, ‘yan bindigar sun kai hari wajen wani taro na aure sannan suka sace amarya.
Sun kuma kashe mutane takwas sannan suka jikkata wasu da dama a garuruwan da aka kai hari sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu.
Harin wanda aka fara shi a daren ranar Asabar ya kai har washegarin Lahadi inda yan bindigar suka kuma sace wasu dabbobi.