Shugaban Ƙasar Malawi Lazarus Chakwera ya ƙwace dukkan ikon da mataimakinsa Saulos Chilima ke da shi bayan wani bincike kan cin hanci ya ambaci sunansa (Saulos) a badaƙalar dala miliyan 150 a kwangilolin gwamnati.
Mataimakin shugaban bai mayar da martani ba zuwa yanzu.
Wani rahoto da hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasar ta fitar ya bayyana sunan jami’an gwamnati na yanzu da waɗanda suka sauka cewa sun karɓi kuɗi daga hannun wani ɗan kasuwar Birtaniya mai suna Zuneth Sattar daga 2017 zuwa 2021, a cewar shugaban.
Hakan na da alaƙa da kwangiloli 16 da rundunonin ‘yan sanda da na sojan Malawi suka bai wa kamfani biyar mallakar Mista Sattar.
Bayan mataimakin shugaban ƙasa, daga cikin mutanen da sunayensu suka fito har da babban sufeton ‘yan sandan ƙasar. In ji BBC.