Gwamnatin Morocco ta bai wa manoma damar shuka tabar wiwi da masana’antu za su yi amfani da su kuma a rika fitarwa kasashen waje a karon farko.
Za a ba manoma a yankunan arewacin al-Hoceima, Chefchaouen da Taounate damar sayar da tabar wiwi don amfani da ita wurin yin magunguna da masana’antu, bisa wata doka da majalisar zartarwar kasar ta amince da ita.
Hukumar da ke sa ido kan magunguna ta kasa, wacce ta amince da matakin, ta ce za a karfafa gwiwar manoma su kara yawan noman wiwi don biyan bukatar kasuwa.
Morocco tana daya daga cikin manyan kasashe masu samar da wiwi ba bisa ka’ida ba a duniya.
Ana nomanta a yankunan da suka fi fama da talauci wadanda ke da tsaunuka a ƙasar Arewacin Afirka kuma ana safarar ta zuwa Turai.
Matakin da gwamnati ta dauka na halasta noman tabar wiwi na nufin inganta yanayin talakawa manoma da samar da kudaden shiga.