Hukumomi a Mozambique na tsare da wasu mutane biyu da aka kama suna kokarin sayar da sassan al’aurar dan Adam kan kudi Kwaca miliyan 35 (dala 42,000).
Rahotanni na cewa sassan jikin na wani mutum ne da aka kashe a yankin Milange na lardin Zambezia mai makwabtaka da kasar Malawi.
Mutanen da aka kama suna safarar sassan jikin su biyu ne, na farkonsu mai shekara 29 da haihuwa ne inda dayan kuma mai shekara 32 ne.
Sun tuntubi wani dan kasuwa a garin kuma sun yi masa tayin “hajar” da suke dauke da ita.
Sai dai dan kasuwan ya sanar da jami’an tsaro wadanda suka yi wa mutanen kwanton bauna.
A halin yanzu suna hannun ‘yan sanda kafin a kai su kotu.
Kwamandar gundumar Milange Alice Evaristo ta ce ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike