Kamfanin dillancin labaran iqna ya tabbatar da cewa, wani jirgin saman Turkiyya ya yi saukar gaggawa a birnin New York na kasar Amurka, yayin da wani matukin jirgin ya mutu bayan da ya yanke jiki ya fadi ya na da tsaka tukin jrgin.
A cewar mai magana da yawun kamfanin jirgin Yahya Ustun, wanda ya rubuta a kan X, wanda a baya Twitter, jirgin ya taso ne daga Seattle, yammacin gabar tekun Amurka a yammacin ranar Talata.
“Matukin jirgin mu na Airbus 350… TK204 daga Seattle zuwa Istanbul ya fadi a cikin jirgin.
“Bayan kokarin ba da agajin gaggawa da bai yi nasara ba, ma’aikatan jirgin na wani matukin jirgin da wani ma’aikacin jirgin sun yanke shawarar yin saukar gaggawa, amma ya mutu kafin ya sauka,” ya rubuta.
Ustun ya kara da cewa matukin jirgin mai shekaru 59 da haifuwa ya yi aiki da kamfanin jiragen sama tun a shekarar 2007, kuma ya yi gwajin lafiyarsa a watan Maris, wanda bai nuna wata matsala ta rashin lafiya ba.