Wani dan majalisa daga jam’iyyar Conservative mai mulki a Biritaniya ya ce yana shirin sauya jinsinsa domin zama dan majalisar dokokin kasar na farko da ya fito fili ya sauya jinsinsa.
Jamie Wallis yana da shekara 37 kuma yana wakiltar wata mazaba ne a Wales.
Ya ce an gano cewa yana fama da matsalar jinsi ta dysphoria, inda yake jin tunaninsa ya bambanta da jinsin da aka haife shi da shi.
Sanarwarsa ta samu sakwanni na goyon baya, inda Firaminista, Boris Johnson, ya yaba wa Mista Wallis saboda jajircewarsa wajen bayyana labarinsa, yana mai cewa babu shakka zai taimaka wa wasu.


