Wannan sabbin kudaden da Dangote ya samu ya saka shi ya samu ci gaba daga matsayinsa na 91 zuwa na 83 cikin jerin attajiran duniya.
Mafi yawancin arzikin Aliko Dangote ya na da alaka ne da kamfaninsa, Dangote Cement Plc, hakan yasa duk lokacin da kudin hannun jarin ya canja sai arzikinsa ya sauya.
Kudin Attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya samu karuwa da Naira biliyan 28.86 (69.4 million) cikin awa 24.
A cewar Bloomberg, arzikin Dangote a yanzu ya kai Dallar Amurka biliyan 20, hakan ya sa ya zama mutum na 83 cikin jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya bayan farfadowarsa daga makon da ya gabata.