fidelitybank

Tirkashi an yi garkuwa da sabon Baturen ‘Yan Sanda

Date:

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi garkuwa da wani jami’in ‘yan sanda reshen shiyya da aka mayar da shi sashin Pankshin na jihar Filato.

An yi garkuwa da sabon Baturen ‘Yan Sandan wato DPO din, wanda ba a iya tantance sunansa a ranar Laraba a otal din da ya sauka a karamar hukumar.

Wata majiya ta shaidawa DAILY POST cewa ‘yan bindigar da yawan gaske, sun mamaye otal din ne da misalin karfe 10:45 na dare, inda suka yi awon gaba da shi da bindiga, suka kuma kai shi inda ba a sani ba.

Ya kara da cewa, “masu garkuwa da mutane sun yi ta harbe-harbe da dama a iska kafin daga bisani su shiga otal din da misalin karfe 10:45 na dare. Ya kasance kamar DPO ne aka yi musu hari; sun harbe shi a kafa kafin a tafi da shi.”

A cewar majiyar, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Filato da sauran jami’an tsaro na cikin dajin da ke yankin suna yin iyakacin kokarinsu na ganin sun kubutar da dan sandan daga hannun wadanda suka sace shi.

DSP Alfred Alabo, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, bai iya tabbatar da sace shi ba, saboda ba a amsa kiran da aka yi a wayarsa.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...

Lauyan Sowore ya bukaci a sake shi cikin gaggawa

Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele...

Najeriya da Indiya za su haɗa kai na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Jihohi 19 da za a yi kwana 9 a na ruwan sama harda Kano – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen za a shafe kwana...

Tinubu ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar matar MKO Abiola

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa...

Abubuwan da Kwamiti ya gano a wajen Kwamishina mai murabus na Kano

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu,...
X whatsapp