Hankula sun tashi a sashen masu haihuwa na Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, bayan da aka sace wani jariri.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa uban jaririn ya ce ƴan biyu matarsa ta haifa a ranar Laraba, sai wata mata ta yi shiga irin ta malaman asibiti ta ce wa matarsa ɗaya daga cikin jariran ba shi da lafiya za a duba shi a wani sashen na asibitin.
Daga nan ta ɗauki yaron ta tafi ba ta sake komawa ba.
Uban jaririn Ibrahim Dallami Khalid ya ce, ya yi tsammanin matarsa ta san matar ne shi ya sa bai yi wata hoɓɓasa ba a lokacin da ya ganta.
“Daga baya bayan na bar asibitin sai matata ta cewa mahaifiyarta ta kawo mata ƙwai. Bayan ta tafi kawo ƙwan ne sai matar ta sake komawa ɗakin ta tambayi surukata ina za ta. Sai ta amsa mata ta wuce.
“Ita kuma matar sai ta yi amfani da damar ta zauna kusa da matata, ta ce mata ɗaya daga cikin jariran ba shi da lafiya za ta kai mata shi sashen da ake duba yara. Sai matata ta ƙyale ta ta ɗauke shi. Tun daga sannan ba a sake jin ɗuriyarta ba.”
Jaridar Daily Trust ta ce ta so jin ta bakin mai jegon amma ba ta cikin hayyacinta tun bayan faruwar lamarin.
Shugaban kwamitin ba da shawara na asibitin Dr. Haruna Liman ya bayyana lamarin a matsayin marar daɗi, kuma rundunar ƴan sandan jihar ta ce tuni ta ƙaddamar da bincike don kama wacce ake zargin.