fidelitybank

Tir da kisan mutane a Barkin-Ladi – Gwamnan Filato

Date:

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, ya yi tir da kakkausar murya dangane da harin da aka kai da ya yi sanadin zubar da jini da ya salwantar da rayukan jama’a a kauyen Heipang da ke karamar hukumar Barkin-Ladi da sanyin safiyar Alhamis.

Wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Gyang Bere ya fitar ta ce gwamnan ya kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a wasu kauyukan karamar hukumar Mangu da aka yi a baya-bayan nan.

Gwamna Mutfwang ya bukaci jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa mutanen da ba su ji ba gani ba gani ba a kauyukan kananan hukumomin Mangu da Barkin-Ladi na jihar.

Ya koka da tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar, ya kuma yi kira da a kara hada kai tsakanin shugabannin al’umma da jami’an tsaro domin kawo karshen hare-haren “marasa hankali”.

Gwamna Mutfwang ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da hadin kai a tsakanin dukkan ‘yan kasa, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, domin samar da zaman lafiya da ci gaban jihar.

Ya ba da tabbacin gwamnati ta himmatu wajen magance matsalolin tare da nuna juyayi ga al’ummomin da abin ya shafa da iyalan wadanda suka mutu.

Ya yi addu’ar Allah ya jikan al’ummar Heipang da Mangu da ke cikin makoki sannan ya bukace su da su yi amfani da cibiyar tsaro da bayanai da gwamnatin jihar ke aiki domin isar da bayanan tsaro domin a gaggauta shiga tsakani domin dakile afkuwar hare-haren nan gaba.

nasarawa news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp