fidelitybank

Tir da Ƴan Ta’addan da suka kashe Masallata a Nijar – Shugaban Pakistan

Date:

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif ya yi alla-wadai da harin ƴanbindiga a wani masallaci da ke garin Kokorou a Jamhuriyar Nijar, inda suka kashe masallata masu dama.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Sharif ya bayyana harin a matsayin “abin takaici”, sannan ya ƙara da cewa “musamman ganin yadda aka kashe mutane suna sallah a watan Ramadan mai alfarma. Wannan ya ƙara nuna cewa ta’addanci ba shi da addini, kuma babu tausayi a ciki,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “a madadin ƴan ƙasar Pakistan, muna alla-wadai da wannan harin na dabbanci, sannan muna taya ƴan Jamhuriyar Nijar baƙin ciki da jaje,” in ji shi.

Rahotanni dai na cewa aƙalla mutum 44 ne ƴanbindiga suka kashe, sannan suka jikkata gommai a harin, wanda suke kai a wani masallaci da ke garin na Kokorou.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp