Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau Juma’a 18 ga watan Yuli, domin ta’aziyyar rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata da ya rasu a ƙarshen watan da ya gabata.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a lokacin da aka yi rasuwar Tinubu ba ya ƙasa, amma duk da haka ya aika tawaga ƙarƙashin ministan tsaron ƙasar domin wakiltarsa a wajen jana’izar.
Tinubu zai kai ziyarar ta’aziyyra ne ga gwamnatin Kano da kuma iyalan marigayin.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana ziyarar a matsayin mutuntawa ga al’ummar Kano da nuna haɗin kan ƙasa, da kuma martaba abubuwan da marigayin ya aikata.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin Kanon ta fitar, gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar su fito domin tarbar shugaban ƙasar bisa tsarin al’adun mutanen Kano.
A ƙarshen watan da ya gabata ne fitaccen ɗan kasuwar ya rasu a wani asibiti a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, aka kuma binne shi a birnin Madina na ƙasar Saudiyya.