Shugaban kasa, Bola Tinubu, zai yi wa ‘yan ƙasar jawabi na sabuwar shekara gobe Litinin, kamar yadda fadar shugaban ta bayyana.
Wata sanarwa ta ce za a yaɗa jawabin shugaban kai-tsaye ta kafofin yaɗa labarai na rediyo da talabijin da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar 1 ga watan Janairu.
“Ana umartar dukkan kafofin yaɗa labarai na rediyo, da talabijin, da na intanet su ɗauki jawabin ta kafar talabijin ɗin ƙasa ta NTA da kuma rediyon tarayya,” in ji sanarwar da kakakin fadar shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar.
Wannan ne bikin sabuwar shekara na farko da Tinubu zai yi a kan mulki bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayu – bayan nasarar da jam’iyyarsa ta APC ta samu a babban zaɓe na watan Fabrairu.