Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ya ce, Bola Tinubu, dan jam’iyyar APC, dan takarar shugaban kasa, zai yi amfani da “sihiri” wajen gyara matsalolin Najeriya idan aka zabe shi a 2023.
Sanwo-Olu ya ce, Tinubu ya san al’amuran da suka addabi kasar nan, domin haka ya zai samar da mafita.
Da yake jawabi jiya a Legas, gwamnan ya ce, ya kamata ‘yan Najeriya su baiwa shugaban jam’iyyar APC na kasa damar zama shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Ya bukaci ‘yan majalisar jihar Legas da su yi kokarin ganin Tinubu ya zama shugaban Najeriya.
Ya ce, “Tinubu ya san al’amuran da suka addabi al’ummarmu kamar bayan hannunsa, kuma ya na da sihirin da zai gyara ƙasar. A cewar Babajide.