Shugaban kasa Bola Tinubu na shirin ganawa da shugabannin ƙasashen duniya a birnin Bissau na ƙasar Guinea domin halartar bikin cikar kasar shekara 50 da samun ‘yancin kai. .
Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce a ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu zai isa Bissau domin halartar bikin da Shugaban Ƙasa Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya shirya.
Kodayake Guinea-Bissau a hukumance ta cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai a ranar 24 ga watan Satumban 2023, an shirya gudanar da bikin a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu zai koma Najeriya kwana ɗaya bayan gama bikin.


