fidelitybank

Tinubu zai tafi Saudiyya kan rikicin Gabas ta Tsakiya

Date:

Yau Lahadi ne ake sa ran shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu ministoci tare da wasu shugabannin hukumomi za su bar Abuja domin halartar taron koli na hadin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulmi wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2024, a babban birnin Saudi Arabia, Riyadh.

Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a birnin a bara.

Taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da tafiyar a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris da kuma shugaban hukumar bayanan sirri ta Najeriya, Mohammed Mohammed.

Sanarwar ta ce ana sa ran a wajen taron Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi a kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa, inda zai jaddada matsayar Najeriya ta neman sasanta rikicin ta hanyar dakatar da bude wuta nan take.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp