Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai sake ganawa da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da na ‘yankasuwa a ranar Alhamis, domin cigaba da tattaunawa kan mafi ƙanƙantar albashi.
Ministan Yaɗa Labarai idris Mohammed ya faɗa wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa jiya Litinin cewa shugaban zai ɗora ne kan tattaunawar da suka fara a makon da ya gabata, inda suka kasa cimma wata matsaya.
Yayin da gwamnatin ta tsaya a kan tayin da ta yi na N62,000, ‘yan ƙwadagon ma sun kafe kan N250,000 a matsayin sabon mafi ƙanƙantar albashin, wanda doka ta ce a dinga duba shi duk shekara huɗu.
Ganawar tasu na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙananan hukumomi ke neman ɓullo da sabon tsarin ba su kasonsu na ƙananan hukumomi 774 a faɗin ƙasar bayan hukuncin kotun ƙoli da ya tabbatar da ‘yancin kashe kuɗinsu da kansu – ba tare da sa-hannun gwamnoni ba


