Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai rantsar da sabbin ministocinsa a ranar Litinin 21 ga wannan wata na Agusta.
Za a rantsar da ministocin ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 10 na safe.
A ranar Laraba ne fadar shugaban ƙasar ta sanar da ma’aikatun da sabobbin ministocin za su riƙe.
Tinubu ya fara miƙa sunan mutum 28 ne ga majalisa don tantance su, a ranar 27 ga watan Yuli, sannan ya ƙara tura mata ƙarin sunayen a cikin watan Agusta.
Majalisar dattawan Najeriyan ta amince da 45 daga cikin mutum 48 da shugaba Tinubu ya aike mata yayin da ta ƙi tabbatar da uku a ciki, da suka haɗa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufai da Stella Okotete daga jihar Delta da kuma Danladi Abubakar daga jihar Taraba.