Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai yi tafiya zuwa ƙasar Faransa a yau Litinin, kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ba a fayyace makasudin ziyarar ba, amma ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya bayan wani dan lokaci kadan.
Wannan ziyarar ta biyo bayan ziyarar da ya kai kasar Equatorial Guinea a baya-bayan nan, inda ya gana da shugaban ƙasar Teodoro Mbasogo, inda suka yi shawarwari, da kuma sanya hannu kan yarjejeniyoyin man fetur da iskar gas, da kuma tsaro.