Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen korar duk wani minista da bai taka kara ya karya ba.
Ngelale ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.
Ya ce shugaban kasar ya fitar da dukkanin ma’aikatun majalisar sa daidai da bukatun ci gaban kasa.
Ngelale ya lura cewa shugaba Tinubu ya sha alwashin tabbatar da kowane minista ya yi aiki yadda ya kamata.
“A shirye yake ya kori minista idan ba ya samun abin da yake so. Tabbas,” in ji shi.
Tinubu ya rantsar da ministoci 45 kwanaki bakwai da suka gabata.


