Kungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta ce, zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai samu aiki mafi wahala a duniya.
Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar ta NEF, ya ce Tinubu zai fuskanci kalubale da dama don tunkarar su.
Tinubu, wanda shine dan takarar jamâiyyar All Progressives Congress, APC, ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa da aka kammala, bayan ya samu kuriâu mafi yawa.
Karanta Wannan:Â Obi ka amince da shan kayin Tinubu – Kayode
Bayan nasarar da ya samu, za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.
Sai dai Baba-Ahmed ya ce Tinubu na fuskantar kalubale a fannin samun amincewar âyan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali.
Da yake rubutawa a shafinsa na mako-mako, Baba-Ahmed ya rubuta cewa: âShugaban da za a rantsar a ranar 29 ga Mayu zai kasance aiki mafi wahala a duniya.
âBabban kalubalensa shi ne samun amincewa. Babu wani shugaba a ko’ina da zai iya cimma wani abu mai kima sai dai idan ya samu isassun ‘yan kasa da za su yarda cewa yana da kyau, kuma yana girmama su.
“Shugaba mai zuwa zai gina nasa ginshikin gwamnati mai nagarta, domin Buhari ba zai bar kowa a baya ba.”