Shugaban kasa, Bola Tinubu, zai bar ƙasar a ranar Laraba 14 ga watan Agusta domin ziyarar aiki ta kwanaki uku a Malabo na kasar Equatorial Guinea, biyo bayan gayyatar da shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ya yi masa.
Ana sa ran ziyarar za ta karfafa alakar diflomasiyya da fadaɗa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
A yayin ziyarar, Tinubu zai gana da shugaba Mbasogo domin tattaunawa da rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da suka shafi man fetur da iskar gas da kuma inganta hadin gwiwar tsaro.
Ana sa ran wadannan yarjejeniyoyin za su karfafa moriyar tattalin arziƙin ƙasashen biyu.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa ne zasu raka sa a ziyarar.
Ana sa ran tattaunawar za ta ba da damar yin hadin gwiwa a muhimman sassa, wanda zai amfani kasashen biyu cikin dogon lokaci.