Shugaban Kasa, Bola Tinubu, zai jagoranci taron addu’o’i na musamman ga tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a Abuja, babban birnin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar ta ce taron – wanda za a gudanar da misalin ƙarfe biyar na maraice agogon ƙasar – zai samu halartar ministocin gwamnatin ƙasar.
Taron – wanda za a gudanar a fadar shugaban ƙasar – zai kuma samu halartar shugabannin majalisun dokoki da wakilai daga fannin shari’ar ƙasar.
Taron addu’ar na zuwa ne bayan addu’ar uku da rasuwar tsohon shugaban da aka gudanar a Daura a gaban tawagar wakilan gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa za a gudanar da taron addu’o’i na musamman ranar Juma’a a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.