Shugaban kasa, Bola Tinubu zai halarci taron ƙasashen Larabawa da Afirka da za a yi a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya, a wani ɓangare na ƙoƙarin da gwamnatin kasar ke yi na jawo hannun jarin kasashen waje ga tattalin arzikin ƙasar.
Mashawarcin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa a Abuja.
“Shugaban zai yi amfani da taron ne wajen jawo hannun jarin kasashen waje kai tsaye zuwa cikin kasar. Taron tabbas zai samar da fa’ida ta fuskar tattalin arzikin ƙasar da Afirka.”
Taron dai na ƙoƙarin zaƙulo fannonin haɗin gwiwa, da samar da ra’ayi bai daya ta fannin ilmi da gogewa, da zayyana ayyuka da tsare-tsare na kyautata alaƙa tsakanin kasashen Larabawa da Afirka.
Taron kuma ya mayar da hankali ne kan tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula da yaƙi da ta’addanci da fatara da ilimi da kiwon lafiya da samar da abinci da bashi da kuma sauyin yanayi.
An gudanar da taron na karshe ne a shekarar 2016. Ngelale ya ce, za a yi cikakken bayani kan tarurrukan da shugaban kasar zai yi da masu zuba jari, waɗanda suka shafi farfado da tattalin arzikin kasar.
Shugaba Tinubu dai zai samu rakiyar ‘yan majalisar ministoci da shugabannin ‘yan kasuwa, inda ake sa ran yin cikakken bayani a yayin ganawarsa da masu son zuba jari.