Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2023, Bola Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar dangane da babban zabe mai zuwa.
Naija News ta rahoto cewa an gudanar da taron ne a ranar Alhamis a gidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja, babban birnin kasar.
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na APC da suka halarci taron sun hada da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara da Simon Lalong na jihar Filato.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole; Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore da tsohon abokin takarar Tinubu, Ibrahim Masari.
A cewar jaridar Nation, taron ya kara dankon zumunci tsakanin dan takarar shugaban kasa, abokin takararsa da shugabannin jam’iyyar.
An fahimci cewa tun bayan da Tinubu ya zama mai rike da tutar jam’iyyar ya na gudanar da taro da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.