Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bada tabbacin gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta maido da zaman lafiya a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato cikin kankanin lokaci.
Shettima ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Juma’a a lokacin da ya ke karbar bakoncin wani basaraken gargajiya daga Mangu, Mishkahan Mwaghavul, John Hirse, wanda ya jagoranci tawagarsa a ziyarar ban girma zuwa ofishinsa da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
A cewarsa, kowane bangare na Najeriya za a ji irin tasirin da gwamnati ke yi a gwamnatin shugaba Tinubu.
Shettima ya ce rikicin da ke faruwa a Filato ba shi da alaka da addini, yana mai jaddada cewa “ya zama wajibi mu fahimci kanmu mu zauna lafiya da juna.”
“Plateau kasa ce mai albarka da Musulmi da Kirista. Abin da ya haɗa mu tare ya wuce abin da ya raba mu.
“Wannan gwamnatin za ta yi amfani da duk wani abu da zai taimaka wajen magance duk wani sabani na siyasa a kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
“Da yardar Allah za mu magance duk wani sabani na cikin gida da ma’anar siyasa da ma kabilanci da ke cikin rikicin da kuma tabbatar da samun mafita mai dorewa,” inji shi.