fidelitybank

Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyara da ya yi

Date:

Fadar shugaban kasa, ta ce shugaban ƙasar, Bola Tinubu zai koma gida yau bayan kwashe kusan mako uku ba ya ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Sanarwar ta ce “Shugaba Tinubu zai dawo yau”.

A ranar 2 ga watan Afurilu ne Tinubu ya fice daga Najeriya zuwa Faransa, a wata ziyarar aiki, kamar yadda sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta bayyana.

Sai dai bayan tafiyar Tinubu abubuwa da dama sun faru a ƙasar waɗanda suka janyo kiraye-kirayen komawar sa.

Hare-hare da aka kai a jihar Filato ta arewa maso tsakiyar ƙasar sun yi sanadiyyar kisan sama da mutum 100, baya ga wanda aka kai cikin makon da ya gabata a jihar Benue wanda shi ma ya kashe sama da mutum 50.

Haka nan wata nakiya da ta fashe kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri ta hallaka aƙalla mutum takwas a jihar Borno, bayan gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya koka da ƙaruwar ayyukan ƙungiyar Boko Haram, wadda ya yi zargin tana karɓe iko wasu yankuna na jihar.

Jagororin adawar siyasar ƙasar, kamar Atiku Abubakar da Peter Obi duk sun soki kasancewar Tinubu a wata ƙasa yayin da Najeriya ke cikin hali na rashin tsaro.

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp