fidelitybank

Tinubu zai bude taron yaki da ta’addanci na Afrika a Abuja

Date:

Shugaban kasa Bola Tinubu zai buɗe taron yaƙi da ta’addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron – wanda Najeriya da haɗin gwiwar ofishin yaƙi da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya – za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu.

Manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Afirka tare da sake fasalin yadda duniya ke kallon ta’addanci a Afirka, da kuma lalubo sabbin hanyoyin magance matsalar a faɗin nahiyar.

Ana sa ran shugabannin gwamnatoci da manyan jami’an gwamnatocin ƙasashen Afirka, da wakilan ƙungiyoyin duniya da cibiyoyi, da jami’an diplomasiyya da ƙungiyoyin fararen hula za su halarci taron.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed za ta halarci taron.

”Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu, da sakataren sashen yaƙi da ta’adancin na Majalisar Dinkin Duniya, Vladimir Voronkov, za su gabatar da jawabai a wurin taron”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp