fidelitybank

Tinubu za mu hadu a kotu ka shirya – LP

Date:

Jam’iyyar Labour Party (LP) mai adawa a zaɓen shugaban ƙasa ta bayyana cewa, za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen da ya bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.

Yayin da yake jawabi a Abuja a yau Laraba, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Datti Baba Ahmed, ya jaddada cewa akwai kura-kurai a zaɓen.

“Mun shiga zaɓen a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP,” a cewarsa. “Kuma za mu ƙwaci haƙƙinmu da sunan LP”.

Tun a ranar Talata jam’iyyun adawa na PDP da LP da ADC suka yi watsi da sakamakon a wani taron haɗin gwiwa, suna masu cewa hukumar zaɓe ta Inec ta gaza saka sakamakon a rumubun IReV da zai sa a gan shi ta shafin hukumar na intanet.

Peter Obi na LP ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri’u 4,223,277, inda Atiku Abubakar na PDP kuma yake biye wa Tinubu da ƙuri’u 6,301,741.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp