Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ƙaddamar da layin dogo na ‘Red line’ na zamani a jihar Legas.
Aikin – mai tsawon kilomita 37 – zai karaɗe wasu manyan yankunan birnin, wanda shi ne cibiyar kasuwancin ƙasar.
Layin dogon na ‘Red line’ ya tashi ne daga Marina ya bi ta unguwannin Yaba da Mushin da Oshodi da Agege, ya dangana har zuwa Ibadan, sannan ya bi har zuwa filin Jirgin Murtala Muhammad.
A shekarar da ta gabata ne dai tsohon shugaban NAjeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da layin dogo na ‘Blue line’ a jihar wanda ya tashi daga Marina zuwa unguwannin Alaba da Mile 2 da Festac da Alajika da jami’ar LASU ya dangana zuwa Maintenance Deport.
Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, shugaba Tinubu ya sake nananta ƙudurin gwamnatinsa na inganta abubuwan more rayuwa a ƙasar.
Shugaban ƙasar ya ce babu gudu, ba ja da baya dangane da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta ƙudiri aniyar aiwatarwa.
Bayan ɗarewarsa kan karagar mulkin Najeriya shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ke biya, da barin kasuwa ta yi halinta dangane da farashin naira, lamarin da ya haifar da tashin farashin man fetur da hauhawar farshin kayayyaki da tsadar rayuwa.