fidelitybank

Tinubu ya ƙaddamar da jiragen yaƙi masu saukar ungulu

Date:

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen mastalar tsaro a ƙasar ta hanyar ƙaddamar da wasu sabbin jirage masu saukar ungulu kirar T-129 ATAK guda biyu da kirar King Air 360ER Beechcraft a barikin sojin saman Najeriy da ke birnin Makurdi a jihar Benue..

Da yake magana ta bakin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar sayen waɗannan sabbin jiragen masu saukar ungulu domin inganta yaƙin da rundunar sojojin saman Najeriya ke yi a ƙasar da yankin yammacin Afirka.

Badaru Abubakar, ministan tsaro ya yaba wa ƙoƙarin shugaba Tinubu na mayar da zaman lafiya a fadin ƙasar, ya kuma gode masa bisa jajircewarsa da goyon bayan da yake bai wa rundunar sojin ƙasar duk da kalubalen da take fuskanta.

Ministan ya jaddada mahimmancin bin jadawali da aiwatar da tsare-tsare masu inganci don tabbatar da kyakkyawan aikin sabbin jiragen da aka sayo, tare da yin daidai da manufar shugaban kasa na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba.

A yayin da yake jaddada mahimmancin wadannan sauye-sauye da aka samu, babban hafsan sojin sama, Hasan Abubakar, ya bayyana shirin rundunar sojin saman Najeriya na kaddamar da sabbin jiragen guda 46 na nau’uka iri-iri a cikin watanni 18 masu zuwa da wani babban sauyin a tsarin tsaron.

Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, duk da cewa NAF na gudanar da ayyukanta ta kowane fanni, ba za ta huta ba har sai ta kawo karshen matsalar tsaro don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƴan Najeriya.

Daga nan, shugaban ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su riƙe imani da fatan ci gaban ƙasar

benue news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp