fidelitybank

Tinubu ya yi tir da tarzomar da aka tayar lokacin zanga-zanga

Date:

Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ake samu yayin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da aka fara a sassan kasar a jiya Alhamis.

Abdul’aziz Abdul’ziz, daya ne daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyar ya sahida wa BBC cewa shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya san ƴan ƙasar na da ƴancin yin zanga-zangar tare da bayyana ra’ayinsu “amman abin takaici yadda aka fito a sassa daban-daban an ɓige da abubuwa waɗanda ba su bane yakamata agani a akan tituna.”

“An ɓuge da cin zarafin marasa galihu da zubar da jini da kuma yin abubuwa na rashin ɗa’a da kuma rashin daidai, wannan abun gwamnati ta yi Allah-wadai da shi, ganin cewa mutanen da basu ji ba basu gani ba, an ƙuntata masu, anyi wa wasu asarar dukiyoyi, har wasu ma sun rasa rayukansu, har ma da jami’an tsaro.” cewar Malam Abdul’aziz.

Gwamnatin Najeriyar ta ce ba ta san wadanda suka shirya zanga-zangar ba, wadanda ake iya cewa gasu kuma ba a Najeriyar suke zaune ba, shiyasa ba za ta iya tattaunawa da su ba.

“Babu wani wanda ya fito, in ba wadanda aka tsinta bisa titi ba, idan mutum bai fito ba ya yi abinda yake cewa shi yayi imani ya yi ba , ta ina zaka zauna dashi, mu bamu taɓa banzatar da koke-koken mutane ba,” In ji Malam Abdul’aziz.

Gwamnatin ta ce ta san halin da ƴan ƙasar ke ciki na matsin rayuwa, sai dai abu ne na ba yadda za a yi, “Ana ƙoƙari aga wane matakai yakamata a ɗauka domin a samu sauƙin wadannan abubuwa.”

Masu zanga-zangar dai na neman gwamnatin Najeriyar ta dawo da tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya sanar da janye shi a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, matakin da gwamnatin ta ce zai yi wahala a iya mayar da tallafin.

“A gwamnatance babu abunda za a ce ba za a iya yi ba, saboda mulkin jama’a ake, amman akwai abubuwan da suke kusan mawuyacin abu ne , yiyuwarsu ɗin akwai wahala, ba dan ba a san yi ba,sai dan dai misali kamar ka ce ka ɗebo ruwa ne daga ƙafaffiyar rijiyar da ba ta da ruwan, saboda babu kuɗin da za a iya amfani da su ayi wannan abun.”

Malam Abdul’aziz ya ce idan mutane sun yi la’akari da abunda ya faru jiya ba lallai su sake fitowa ba ” ai gani ya kori ji idan har mutane suka ga abunda suka faru jiya Alhamis a garuruwa daban-daban,kace kuma wai zaka sake yin zanga-zanga, to bana jin anyi aiki da hankali.”

the sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp