Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Juma’a tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari sun yi sallar Juma’a.
An gudanar da sallar ne a masallacin Aso Rock dake fadar shugaban kasa, Abuja.
Sallar dai ta gudana ne karkashin jagorancin Babban Limamin Masallacin Malam Abubakar Sulaiman.
Wanda suka halarci sallar, sun hada da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Doguwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen. Babagana Monguno.
Sauran sun hada da babban lauya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da wasu shuwagabannin kungiyoyin sa-kai na soja da sauran musulmin muminai.