Ƙaramin minstan gidaje na Najeriya Abdullahi T Gwarzo ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi ƙoƙari wajen daidata lamurran ƙasar nan duk da cewa babu wadatar kuɗi.
Gwarzo na wannan bayani ne yayin da gwamnatin Tinubu ke cika shekara ɗaya a kan karagar mulki.
A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ne aka rantsar da Tinubu bayan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, sai dai ya karɓi mulkin ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale masu yawa.
Bayan karɓar mulkin nasa tattalin arziƙin al’umma ya ƙara taɓarɓarewa sanadiyyar tashin farashin kaya, wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da kuma faɗuwar darajar naira.
Sai dai Gwarzo ya ce “ai duk wanda ya san yadda aka zo aka samu ƙasar, ya ga kuma yadda ake ciki yanzu…an ci ƙarfin aiki, kullum ci gaba ake samu.”
Ya kuma ce gwamnatin ƙasar na gina gidajen masu ƙaramin ƙarfi a faɗin Najeriya waɗanda za a kammala a cikin wata uku.