Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya haɗu da fuskokin da ya daɗe da sani a gida wajen ƙasar a wurin bikin rantsar da sabon Shugaban Ƙasar Ghana John Mahama.
Tsofaffin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan na cikin mutanen da ya yi musabaha da su a wurin bikin.
Kazalika, ya haɗu da shugaban Ghana da ya bar gado, Nana Akupo-Addo a birnin Accra a yau Litinin.
“Ba ni da wata tantama gwamnatin John Mahama za ta kawo sauyi mai albarka,” in Tinubu yayin jawabinsa a wurin biki.