fidelitybank

Tinubu ya yi gum da baki akan takun sakar shugaban majalisa ta 10

Date:

A yayin da ake ci gaba da takun-saka a kan shugabancin majalisar wakilai ta 10, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi watsi da yiwuwar sake maimaita maganar majalisar ta 8 a lokacin da ‘yan adawa suka fi karfin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), kan shugabancin majalisar dokokin kasa.

Tinubu, wanda mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kudu maso Yamma, Isaac Kekemeke, ya wakilta, ya bayyana hakan a yayin taron lacca da aka shirya domin karrama shugaban kungiyar ta Afenifere, Cif Reuben Fasoranti, wanda ya cika shekaru 97 a karshen mako.

A cewarsa, har yanzu jam’iyyar na da isasshen lokacin da za ta hada bangarorin da ke rikici da juna kafin kaddamar da majalisar dokokin kasar.

Ya kawar da fargabar cewa ‘yan adawa za su yi awon gaba da shugabancin majalisar dokokin kasar.

“Yan adawa ba za su mamaye Majalisar Dokoki ta kasa ba; Shugaban kasa da jam’iyya mai jiran gado suna aiki tukuru don ganin cewa duk abin da kuka ga a matsayin fushi za a warware shi, kuma wannan dimokuradiyya ce,” inji shi.

A makon da ya gabata ne jam’iyyar APC ta amince da Sanata Godwill Akpabio da Tajudeen Abbas a matsayin shugaban majalisar dattawa kuma kakakin majalisar wakilai.

Tun a wancan lokaci masu neman shugabancin NASS na 10 suka yi barazanar kauracewa jam’iyyar.

A shekarar 2015, Bukola Saraki da Hon Yakubu Dogara sun yi nasarar lashe zaben shugabancin majalisar dokokin kasar ba tare da bukatar jam’iyyar APC mai mulki ba.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp