Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya gwamnati da al’umar Laberiya murna kan samun nasarar kammala zaɓen shugaban ƙasar cikin kwanciyar hankali.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, ya fitar, shugaba Tinubu ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Joseph Boakai,murnar lashe zaɓen, tare da yin kira a gare shi da ya haɗa kan ‘yan ƙasar wajen gudanar mulki don samar wa ƙasar ci gaba.
Haka kuma shugaban na Najeriya ya jinjina wa shugaban Laberiya, George Weah, bisa nuna abinda ya kira “tattakun shugabanci da ba kasafai ake nuna irinsa ba” ta hanyar karɓar faɗuwa domin kauce wa rikici a ƙasar.
“Abin da shugaba Weah ya yi babban abin misali ne a tsarin dimokradiyya a wannan lokaci musamman a yankin Afirka ta Yamma, inda dimokradiyya ke fuskantar barazanar masu ƙwace wa mutane abin da suka zaɓa”, in ji Tinubu
“Haƙiƙa na jinjina wa shugaba George Weah bisa halin kima da dattaku da ya nuna. Ya nuna cewa bai kamata sakamakon zaɓen ya zama silar tashin hargitsi a ƙasar ba,” in ji shugaban na Najeriya.
Yarda da faɗuwa tare da taya abokin hamayya murnar lashe zaɓe, ba abu ne da aka saba gani ba a nahiyar Afirka, inda galibi waɗanda suka sha kaye kan garzaya kotu don neman haƙƙinsu, bisa zargin aikata maguɗi a zaɓukan da suka sha kayen.