fidelitybank

Tinubu ya umarci Sojoji su tabbata sun kawo karshen ‘yan Ta’adda a 2025 – Matawalle

Date:

Karamin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umurci sojojin Najeriya da su tabbatar an kawo karshen ayyukan ta’addanci a 2025.

Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a gidansa da ke Gusau, inda ya tabbatar da cewa sojoji za su yi duk abin da ya dace domin bin umarnin shugaban kasa.

Da yake magana, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ce gwamnatin tarayya ta kammala dukkan shirye-shiryen tura karin sojoji da kayan aikin soji zuwa yankunan da ake fama da rikici a shiyyar Arewa maso Yamma.

“Gwamnatin tarayya da shugabannin sojoji sun damu matuka game da batun masu ba da labari na taimaka wa ‘yan fashin.

“Wannan shine babban kalubalen rashin cin nasara a yakin da ake yi da ‘yan bindiga,” in ji shi.

Matawalle ya koka da yadda masu ba da labarin ’yan uwa ne da ke sayar da lamirinsu ga shaidan don neman kudi.

Hakazalika, ministan ya gargadi ‘yan siyasa da su daina cakude siyasa da batun tsaro.

breaking news in nigeria today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp