Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta gudanar da bincike domin musabbabin turmutsutsun da ya auku a jihar Oyo, wanda ya yi sanadiyar mutuwar yara da 35 da jikkata wasu a wurin taron al’ada na ya yara.
Tinubu ya bayyana wannan buƙatar ce a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar.
Shugaba Tinubu ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa, sannan ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamanti da iyalan waɗanda abin ya shafa, da al’ummar jihar baki ɗaya.
“Kula da yaranmu nauyi ne da bai kamata a yi wasa da shi ba,” in ji shi, sannan ya ƙara da kira ga masu shirya taruka da su riƙa kula hanyoyin gudanar da tarukansu cikin tsanaki.
A ranar Alhamis, ƴansanda sun ce sun kama mutum bakwai da suka da alaƙa da shirya taron da ya janyo turmutsutsun, ciki har da wadda ta shirya taron, tsohuwar matar Ooni na Ife Naomi Silekunola.
Wasu iyayen da suka zanta da ƴanjarida sun ce sun raka yaransu taron ne domin an yi alƙawarin za a raba kuɗi naira 5,000 ga duk wanda ya je, sannan za a raba abinci kyauta.