fidelitybank

Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Date:

Shugaban kasaa Bola Ahmed Tinubu, ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye.

Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba.

Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Same wato iyakar Najeriya da janhuriyar Benin.

Ambasada Nuhu ya ce “hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al’umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma”, in ji shi.

“Mun ji dukkan ƙorafe-ƙorafen da ake yi kan hanyar na yadda shingayen da jami’an tsaro da na jami’an hana fasa ƙauri ke sanyawa ke shafar matafiya da kayan da masu shigowa ko fitar da kaya.

Shugaban hukumar Ecowas Omar Alieu Touray ya yi, Allah wadai kan yadda jamai’an tsaron da ke kula da shingayen da ke hanyar ke ƙarɓar kuɗi a hanun al’ummar ƙasashe daban-daban da ke shige da fice a ƙasar, wanda ya ce hakan, ya saɓa da shirin ECOWAS na haɗe yankin wuri ɗaya

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rikicinta da Cambodia na iya rikidewa ya koma yaƙi – Thailand

Thailand ta gargaɗi cewa rikicinta da Cambodia na iya...

Isra’ila da Amurka sun soki Faransa na amincewa da kafuwar ƙasar Falasɗinawa

Isra'ila da Amurka sun yi Allah-wadai da matakin da...

Najeriya za ta kwashe ma’aikatan ta a Congo – Tugar

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta na shirin kwashe...

Ministan harkokin jin ƙai ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Ministan harkokin jin kai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya zama...

Amurka za ta lalata magungunan takarar haihuwa na dala miliyan 10 da za a kawo Afrika

Gwamnatin Amurka na shirin lalata magungunan tazarar haihuwa da...

Hukumar NAFDAC ta kama abubuwan fashewa a Kano

A cewar hukumar, an gano lita 60,000 na sulphuric...

Sojoji sun fafata da da ‘yan Bindiga a Neja

Rundunar sojiji ta ce, sojoji tare da haɗin gwiwar...

Majalisar Dinkin Duniya za ta dakatar da tallafin abinci a Najeriya

Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya bayyana...

Tinubu ya na murkushe ‘Yan adawa – Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce...

Gwamnatin Kano ta baiwa yara fifiko – UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya...

Majalisar ta amince da buƙatar Tinubu na ciyo bashin dala biliyan 21

A ranar Talata ne majalisar Dattawa ta amince da...

An sallami Gwamnan Katsina daga asibiti bayan ya samu rauni a hatsarin mota

An sallami gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda,...
X whatsapp