fidelitybank

Tuntubi ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana murnar lashe zaɓe

Date:

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya taya zababben shugaban kasa John Dramani Mahama murnar nasarar da ya samu a babban zaben kasar Ghana da aka gudanar ranar Asabar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

A cewar sanarwar, Tinubu a wata tattaunawa da ya yi da Mahama ta wayar tarho, ya bayyana fatan cewa hawan sa kan karagar mulki a karo na biyu zai kara kawo zaman lafiya a kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS.

Tinubu ya yabawa al’ummar Ghana bisa jajircewarsu na tabbatar da dimokradiyya.

A cewarsa, an nuna hakan ne ta hanyar gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki cikin lumana da nasara.

Tinubu ya yabawa ‘yan Ghana bisa sake nuna wa duniya cewa dimokuradiyya ita ce hanyar da aka fi so wajen samun kwanciyar hankali a siyasance, ci gaban tattalin arziki, adalcin zamantakewa da gudanar da mulki cikin gaskiya a Afirka.

Ya tabbatar da cewa amincewar Najeriya da yankinsu kan ka’idojin ‘yancin jama’a na zaben shugabanninsu cikin ’yanci zai kasance abin alfahari.

Shugaban na Najeriya ya yabawa Dr Mahamudu Bawumia, dan takarar jam’iyyar New Patriotic Party (NPP) da mataimakin shugaban kasar Ghana, bisa amincewa da shan kaye kafin hukumar zaben Ghana ta bayyana a hukumance.

Tinubu ya ce matsayin Bawumia ya karfafa tsarin dimokradiyyar Ghana.

Ya ce komawar Mahama gidan Jubilee, bayan da ya rike mukamin shugaban kasa daga shekarar 2012 zuwa 2017, ya nuna amincewar al’ummar Ghana ga shugabancinsa da kuma hangen nesansa na kai kasar ga wani matsayi mai girma.

DAILY POST ta ruwaito cewa Mahama ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasar Ghana daga shekarar 2009 zuwa 2012, dan majalisar wakilai daga 1997 zuwa 2009, ya kuma rike mukamai na mataimakinsa da minista tsakanin 1998 zuwa 2001.

“Shugaba Tinubu ya sake sabunta cikakken goyon bayansa na zurfafa dankon zumunci tsakanin Najeriya da Ghana wanda tarihi ya gindaya, alakar al’adu, goyon bayan juna da hadin gwiwa, manufofin kasashen Afirka, dimokuradiyya, bin doka da oda da kuma hadewar tattalin arziki.

“Shugaban Najeriya ya gode wa shugaba Nana Akufo-Addo saboda kyakkyawan jagoranci da kuma gudummawar da ya bayar ga ci gaban Ghana da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Sanarwar ta ce “Shugaban yana fatan yin aiki tare da gwamnatin shugaba Mahama mai jiran gado don karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu a bangarori daban-daban da kuma samar da makoma mai haske a yankin yammacin Afirka.”

www nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp